Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya doke Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa da aka yi a mazabar Makarantar Islamiyya na JNI Nizamiyyah dake garin Tambuwal.
Ita dai mazabar JNI Nizamiyyah, ita ce mazabar gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Jam’iyyar APC ta samu kuri’u 439 ita kuma PDP ta samu 444.