Atiku ya doke Buhari a mazabar Saraki

0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya doke Shugaba Muhammadu Buhari a mazabar shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki dake Ilori.

Sakamakon zaben ya nuna cewa Atiku ya samu kuri’u 219 shi kuma Buhari ya sami kuri’u 68.

Shugaban majalisar dattawan, Bukola Saraki ya lashe na sa zaben inda ya doke abokin karawar sa na jam’iyyar APC.

A sakamakon zaben majalisar dattawan ya nuna cewa PDP ta sami kuri’u 269 ita kuma APC ta sami kuri’u 59.

Bayannan PDP ta sami kuri’u 255 ita kuma APC kuri’u 40 a wasu mazaban dake yankin mazaban Saraki din.

Share.

game da Author