APC ta yi mana rashin adalci a Zamfara -Yari

0

Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, ya bayyana cewa uwar jam’iyyar APC ta kasa, ta yi wa al’umar Zamfara magoya bayan jam’iyyar rashin adalci.

Yari ya yi wannan furucin ne a cikin wani faifan bidiyo da PREMIUM TIMES ta ruwaito shi ya na hira da manema labarai a Abuja.

Sai dai kuma ya kara da cewa duk da ran su ya baci, sun yafe wa APC rashin adalcin da ta yi musu.

Cikin bidiyon dai Yari ya rika kawo ayoyi daga cikin kundin dokokin Najeriya da ya ce sun nuna halascin zaben fidda gwanin da ya gudanar na APC a Zamfara.

Bayan nan kuma ya sake buga misali da yadda aka fitar da sunan Shugaba Muhammadu Buhari a takarar shugaban kasa, a ka ce an amince shi ne dan takara.

Yari ya ce duk da haka an bi kananan hukumomi da jihohi an yi layin tabbatar da Buhari, sannan aka zo Abuja aka jaddada shi.

A kan haka ya ce ashe kenan su ma abin da suka yi a Zamfara daidai ne kenan.

Gwamnan wanda wa’adin sa ke karewa cikin watan Mayu, ya yi wa jihar fatan alheri da kuma fatan samun shugabanni nagari.

INEC ta yi amfani da rahoton uwar jam’iyya wanda ya ce ba a yi zaben fidda gwani a Zamfara ba, ta hana jam’iyyar shiga takara.

Cikin makon shekaranjiya kuma Kotun Tarayya ta jaddada haramcin APC shiga takara a Zamfara.

Share.

game da Author