Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashe mazabar say zaben shugaban kasa Inda ya samu kuri’u 523.
Shi kuwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP ya tashi ne da kuri’u uku kacal a wannan mazaba.
Sai dai Kuma APC an yi raga-raga da Jam’iyyar APC a zaben majalisar dattawa, Inda ba PDP ba Jam’iyyar Accord Party ce ta lashe zaben wannan mazaba.
Lawal Nalado na Jam’iyyar Accord Party ya doke Ahmad Babba-Kaita na APC.
Nalado ya samu kuri’u 262 shi Kuma Ahmad ya samu kuri’u 247.
Discussion about this post