Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana Gwamna Abdul’aziz Yari na Zamfara a matsayin wanda yayi nasara a zaben Sanata na Zamfara ta Yamma da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ya ruwaito cewa Yari ya yi nasara a Kananan Hukumomin da suka kunshi Anka, Bakura, Bukkuyum, Gummi, Maradun da Talatan Mafara.
Da ya ke bayyana sakamakon zaben, jami’in zabe Lawal Mayanchi ya ce Yari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 153,626, shi kuma Lawal Hassan na PDP ya samu 69,293.
Ana saura kwana uku zabe ne Kotun Daukaka Kara ta sahale wa Zamfara cewa za ta iya shiga zabe.
A baya Babbar Kotun Tarayya ta goyi bayan INEC da ta haramta wa Zamfara shiga zaben gwamna, majalisar tarayya da na jihohi.