Zabe mai zuwa zai zama zakaran gwajin dafi a wajen ‘yan Arewacin Najeriya. Za a gudanar da za6en tsakanin dattijai guda biyu daga addini daya, yanki daya, kabila daya.
Tsakanin shugaba Buhari da Atiku kowa jinsin fulani ne kuma daga Daular Usmaniyya wacce aka fi sani da Arewacin Najeriya. Dukkaninsu jinin yakin Mujaddadi ne Shehu Usmanu Danfodio (Rahimahullah).
Cikin ikon Allah sai ya kaddara kasancewarsu ‘yan takarkarun kujerar shugabancin kasar Najeriya. Kamar dai yadda mai karatu ya Sani Buhari ne shugabantar kasar tun bayan karbe mulkin da yayi a hannun shugaban kasa mai ci daga jam’iyar PDP a shekara ta dubu biyu da sha biyar.
Shi kuma Atiku, shine tsohon mataimakin shugaban kasa a lokacin mulkin Obasanjo na zango biyu a jere.
Gaskiya ina jiye wa ‘yan Arewacin Najeriya, lallai yakamata su yi abun kwarai a zaben bana saboda kowa ya zira musu ido su ci junansu. Duk sanda muka gudanar da zabe cikin rikici da karya doka ta hanyar yin abun Allah-wadai, to babu shakka mun kara rusa kanmu a idon duniya. Dama wasu suna ta rubuce-rubuce suna ce mana talakawa da jahilai, to kun ga kai-tsaye sai su samu hujja akan abun da suke fada.
Mu tsaya tsayin-daka da addu’a mu zabowa kanmu alheri saboda rayuwarmu ta gaba a Najeriya. Kowanne a tsakanin Buhari da Atiku ya samu dama an ganni, don haka kowa za a iya gwada nauyinsa da ayyukansa na alheri. Dan siyasa ko kansila ya taba yi za a iya gwada nauyinsa idan yazo yana neman kujerar gwamna.
Babbar matsalarmu son zuciya, shiyasa muke ta shan wuya a siyasance. Kowa a cikinmu yayi imani da jam’iyarsa, idan ba ita ba sai rijiya koda ba ta da ‘yan takara na kwarai.
Jam’iya dai ba mutum bace, ingancinta yana da alaka da mutanen cikinta saboda haka ko kaine Herbert Marculay a Najeriya Wanda ya fara qirqiro jam’iya ta NCNC a 1920 ka hakura da ita ka duba cancanta don cigaban kanka da na jama’a baki daya. Mun dade muna bautawa jam’iya a Najeriya, sai mu gwada bautawa nagarta da dacewa a zaben bana.
Ban cewa kowa ya zabi wani ba, amma duk mutumin da yake da tunani fiye da nawa yasan abun da ya dace wanda zai kawowa al’umma mafita. Ni har na jiyo kanshin sabuwar Najeriya ma insha Allah.
Ku hadu da ni Comrade M.K Soron dinki a cikinta.
Allah ya zaba mana mafi alheri cikin iyawarsa