Kotun Daukaka Kara a Abuja ta jingine hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yi, inda a yau kotun ta bada izinin cewa jam’iyyar APC na da damar fito da ‘yan takara a zaben 2019 a Jihar Zamfara.
Idan ba a manta ba, a ranar 25 Ga Janairu ne Babbar Kotu a karkashin Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, ta ce INEC ta yi daidai da ta hana jam’iyyar APC fitar da ‘yan takara a Jihar Zamfara, saboda ba a yi zaben fidda-gwani a jihar ba.
Sai dai kuma a wani hukunci da wani gungun alkalai suka zartas yau Alhamis a Abuja, a bisa jagorancin Babban Mai Shari’a Abdul Aboki, Kotun Daukaka Kara ta jingine wancan hukunci.
Kotun Daukaka Kara ta amince da lauyoyin APC, wadanda suka ce an maka jam’iyyar kara kotu ne a lokacin da wa’adin kai karar ya wuce.
Kamar yadda alkalan suka nuna, sun ce kamata ya yi a shigar da kara, akalla kwanaki 14 daga ranar da aka yi zargin cewa an yi ba daidai ba.
Dangane da haka ne sai Kotun Daukaka Kara ta ce shigar da karar da aka yi bayan kwanaki 14, ya nuna cewa waccan kotun ba ta da hurumin da ma za ta tsaya ta saurari karar.
“Don haka kotu ta soke wancan hukunci saboda babu hurumin da zai sa waccan kotu ta saurari karar har ta yanke hukunci a kai.” Inji Kotun Daukaka Kara.
Discussion about this post