An kayar da Saraki a Daya Daga Cikin Kananan Hukumomi Hudu

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya sha kaye a karamar hukuma daya daga cikin kananan hukumomi hudu da ya ke wakilta daga jihar Kwara.

Saraki mai takara a karkashin PDP, ya rasa karamar hukumar ce ga dan takarar APC, Ibrahim Oloriegbe.

Yayin da aka kammala tattara sakamakon karamar hukumar Asa, kuma aka sanar, har zuwa yau Lahadi da ran aba a kammala tattara na sauran kananan hukumomin uku ba.

Sanarwar da INEC ta bayar a yau Lahadi da rana, ta ce Saraki ya tashi da kuri’u 11,252 a karamar hukumar Asa, yayin da dan takarar APC kuma ya lashe kuri’u 15,923.

Haka jami’in INEC ya bayyana cewa ana jiran sakamakon sauran kananan hukumomin shiyyar uku.

Share.

game da Author