An kashe mutane 16 a arangamar mahara da ‘yan banga a jihar Sokoto

0

Kakakin ‘yan sandan jihar Sokoto Muhammad Sadiq ya bayyana cewa wasu mahara sun kashe mutane 16 a karamar hukumar Raba.

Sadiq ya bayyana haka wa PREMIUM TIMES a daren Talata inda ya kara da cewa maharan sun far wa kauyen Yawuri dake karamar hukumar Raba da misalin karfe biyu na safiyar Talata inda suka yi garkuwa da mutane shida a kauyen.

Wadanda akayi garkuwa da sun hada da Ayuba Tali, Mamman Yawuri, Musa Usman, Kamusho Yawuri, Atta Yawuri da Illiya Tali. Ba a dade da tafiya dasu Illiya Tali ya sulale ya gudu daga inda aka ajiye su.

‘‘Bayan gari ya waye wasu ‘yan banga dake kauyen suka fantsama dajin domin nemo wadannan mutane. An yi barin wuta tsakanin maharan da ‘yan banga inda har aka kashe mutane 16.

Sadiq yace akwai yiwuwar cewa sauran burbudin maharan da suka yin garkuwa da mutane ne a jihar Zamfara suka yi hijira zuwa wasu bangarorin jihar Sokoto.

Ya ce duk da haka rundunar za ta yi iya kokarinta wajen ganin ta kamo wadannan mutane.

Share.

game da Author