Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta Kama wani mutumi mai suna Prince Chinecherem da laifin danne wani yaro mai shekaru 13 ta dubura.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imohimi Edgal ya sanar da haka ga yake zantawa da manema labarai.
Edgal ya ce a dalilin wannan abu da Prince yake yi da wannan yaro, yaran ya Kamu da cutar kanjamau.
” Wannan abin takaicin ya faru ne a Ejigbo ranar 22 ga watan Janairu.
” A Wannan ranar makwabtan Prince ne suka Kama wannan yaro yayin da yake sanda yana kokarin ya gudu.
” Da suka damke shi sai suka tambaye shi me ya kai shi dakin Prince. Sannan suka bude wani bakar leda dake hannun sa sai suka ga kwaroro roba ne da aka riga aka yi amfani da su da dama a ciki.
Edgal ya ce bayan an kawo Prince da wanna yaro ofishin su ne aka yi musu gwaji a asibiti.
Ya ce sakamakon gwajin ya nuna cewa an dade ana lalata da wannan yaro ta baya sanna dukkansu na dauke da cutar kanjamau.
Edgal ya ce za a kai Prince kotu da zarar sun kammala bincike.
Discussion about this post