An bindige shugaban APC a Jihar Benuwai

0

Wasu ‘yan bindigar da ba a gane ko su wa ba ne, sun bindige Shugaban Jam’iyyar APC, reshen Karamar Hukumar Ohimini da ke cikin Jihar Benuwai.

An harbe Boniface Okoloho ne a jiya Asabar a lokacin da ya ke kan hanyar sa zuwa gida, bayan da ya ke barin wani wurin taron jam’iyya da ya halarta a Ohimini.

Yankin Ohimini, yanki ne da kabilar Idoma suka yi kaka-gida, kuma ya na daya daga cikin bangaren da suka hadu suka yi Shiyyar Sanatan Benuwai Ta Tsakiya.

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Olubunmi Oshoko, ya tabbatar da cewa an kai wannan rahoton daga waccan karamar hukumar.

“Ba zan iya hakikancewa ba, amma dai na san an kawo rahoton kisan wani dan siyisa, amma ban tantance ko daga ina ne aka kawo rahoton ba.”

Sai dai kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Benuwai ta Kudu, Mohammed Hassan, ya tabbatar wa wakilin PREMIUM TIMES da kisan da aka yi wa Boniface.

Ya ce jam’iyyar su za ta yi karin bayani dangane da kisan nan ba da dadewa ba.

A jiya ne dai aka zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa zuwa ranar 23 Ga Fabrairu, bayan jinkirin da aka dan samu saboda wasu dalilai da suka hada har da tashe-tashen hankula da kona motocin zabe.

Share.

game da Author