An babbake motocin APC 9 a wajen Kamfen a Abuja

0

A wani turmutsitsi da ya kaure a Abuja tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC da PDP, wasu matasa sun babbake motocin Kamfen din APC har 9 a daidai hanyar su ta zuwa fadar sarkin Jiwa dake unguwan Dei-Dei a Abuja.

Suma matafiya basu sha da dadi ba domin kuwa an farfasa musu motoci.

Kamar yadda Kamfanin Dilancin Labaran Najeriya ya ruwaito, su dai masu Kamfen suna hanyar su ne na zuwa Fadar sarkin Jiwa kawai sai suka iske an kakkafa shingaye a hanyoyin kusa da Kasuwar Katako da ke Dei-Dei.

Anan ne fa wasu matasa suka firfito dauke da bamabamai fetur a kwalabe suka rika jejjefa wa wadannan jerin motoci na Kamfen. An sanar cewa babu wanda ya sami rauni a wannan harin sai dai an tafka hasara.

A dalilin Jami’an tsaron da ke tare da wadannan masu yawon Kamfen ne ya sa abin ya zo da sauki domin sun rika harba bindigogi sama domin tarwatsa wadannan matasa da suka yi dafifi a titin suna jiran isowar masu kamfen din.

Shugaban APC na Abuja, Musa Muhammed ya bayyana cewa wannan abu da ya faru nuni ne cewa lallai sai jami’an tsaro sun maida hankali a lokacin zabe matuka domin da a lokacin Zabe ne da abin ya fi haka muni.

Share.

game da Author