Ambaliyar Daloli, Goguwar Kwankwaso, Bindige Barawon Akwati, Ko zasu canja ra’ayin masu zabe?
DAGE ZABE
Dage zabe da aka yi daga ranar 16 zuwa 23 Ga Fabrairu, ya zo da sabuwar dawurwura a tafiyar takarar kujerar Shugaban Kasa. Dukkan manyan kungiyoyi biyun, wato APC da PDP na zargin juna wajen yi wa shirin gudanar da zaben kafar-ungulu.
BINDIGE BARAWON AKWATI
Furucin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a ranar Litinin a taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC a Abuja, inda ya ce duk wanda ya saci akwatin zabe, za a bindige shi, ya janyo masa tsangwama sosai. Ko da ya ke dai magoya bayan sa da ba su taba ganin laifin sa, su na ganin daidai yayi.
Buhari ya manta cewa dokar zabe ta ce a daure barawon akwati tsawon watanni 24. To shi kuma ya fito ya ce a kashe. Hakan ya sa masu adawa na ci gaba da tuna wa jama’a irin mulkin kama-karyar da a baya suka rika zargin Buhari na yi.
Wannan furuci kuma zai kara sa masu sa-ido daga kasashen waje su kara sa ido a kan Buhari sosai da sosai.
KARFIN GUGUWAR KWANKWASIYYA
Kafin fara kamfen, da dama a kasar nan na tunanin cewa hasken fitilar Sanata Rabi’u Kwankwaso ya dusashe. Na farko dai saboda shafe shekaru uku da ya yi bai shiga Kano ba, saboda gudun barkewar rikici tasakanin magoya bayan Kwankwasiyya da na Gwamna Abdullahi Ganduje.
Na biyu kuma Kwankwaso ya samu matsala wajen fidda dan-takara, inda da dama daga manyan na kusa da shi da ke son kujerar gwamna, ba su samu ba, sai Abba Kabiru Yusuf. Wannan ya sa duk suka koma APC, wasu kuma PRP.
Kwankwaso yaba duniya mamaki ganin yadda ya farfado da PDP a jihar Kano, har ta zama abin tsoro ga Buhari da APC da kuma Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje.
A yanzu ana ganin Kwankwaso shi ne madugun PDP a Arewa da ma Najeriya gaba daya.
TSOMA KAFAR MALAMAI CIKIN SIYASA
Sabuwar guguwa ta barke a Arewacin kasar nan, inda malaman addinin musulunci na bangaren Kungiyar Izala su ka yi kane-kane a sha’anin goyon bayan dan takara. Yayin da wasu ke “Sai Buhari”, wasu kuwa sun rikka yin kururuwar “Sai Atiku”.
Sai da ta kai kowane bangare na jawo nassin cancantar wanda su ke goyon baya. Guwawar ta yi zafi sosai yayin da Sheikh Abubakar Gero ya tsine wa wanda ba ya goyon bayan Buhari. Sai dai kuma ganin yadda ya rika shan caccaka, daga baya ya fito ya nemi afuwar jama’a, aka yafe masa.
SIYASAR RABA KAN ‘YAN FIM DA MAWAKA
Su ma ’yan fim na Hausa kan su ya farraka a wannan lokacin kamfen. Kamar yadda su ma mawakan Hausa na su kan ya rarrabu. Ali Nuhu da wasu ‘yan fim da dama sun a bangaren Buhari. Haka Rarara da wasu masu mawaka duk su na bin Buhari.
A bangaren Atiku kuwa, Sani Danja da Adamu Zango da wasu da dama wadanda suka dawo daga rakiyar Buhari, duk sun koma bayan Atiku. Amma Mansura Isa, matar Sani Danja, ta na cikin zugar magoya bayan Atiku.
HANA APC SHIGA ZABEN RIBAS DA ZAMFARA
Hakan zai rage wa APC kazar-kazar a jihohin biyu, kuma zai sa ta rasa kuri’u da dama, duk da dai ba a hana ta shiga zaben shugaban kasa ba. Duk dan takara zai so a ce ya rike jihar Rivers idan ya zama shugaban kasa, saboda ita ce jihar da ta fi kowace karbar kason kudade daga hannun gwamnatin tarayya, ita da Akwa Ibom.
Sauran abubuwan da suka yi tasiri a yakin neman zaben Atiku da Buhari, sun hada da zuwan Atiku Amurka, wanda hakan ta sa kaffara ta kama da dama daga magoya bayan Buhari da suka rika rantsuwa cewa bai isa ya je Amurka ba.
Akwai kuma batun saurin dimuwar da Buhari ya rika yi a wurin kamfen, inda ya rika ambatar mukaman da ba su ne zai bayar da tuta ga masu takarar su ba. Sai kuma yadda a Kudu ake yawan nuna bangarancin Buhari inda ya rika nada manyan jami’an fannonin tsaro duk ‘yan Arewa.
ASKI YA ZO GABAN GOSHI
PREMIUM TIMES HAUSA na mai hasashen cewa dukkan su biyu din, Atiku da Buhari kowa zai iya cin zaben 2019. Kuma duk wanda ya yi nasara daga cikin su, ba za a yi mamaki ba, saboda ya na da karfin magoya bayan da za su jefa masa kuri’a.
Ba kamar zaben 2015 ba, inda guguwar Buhari ta yi wa jam’iyya mai mulki a lokacin mummunar barna.
AMBALIYAR DALOLI
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka kan yadda Daloli da kudaden Kasashen wake suka karade kasar nan a dan Kwanakin nan.
Buhari yace yaduwar wadannan kudade a kasarnan a daidai lokacin Zabe da muke ciki makirci ne da wasu suka shirya domin su siya kuri’u daga hannun mutane ko da karfin arzikin su.
MURABUS DIN OSINBAJO
Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai ya yi murabus daga kujerar mataimakin shugaban Kasa bisa dalilin wai kin gayyatar sa taron majalisar tsaro ta kasa da aka yi.
Discussion about this post