Malaman kiwon lafiya sun bayyana cewa ciwon Sankara ko kuma daji cuta ce dake kama kowane bangaren jikin mutum da idan ba an gaggauta neman magani ba ya kan yi ajalin mutum.
Wata sa’a cutar kan bullo jikin mutum kamar kumburi ko kuma kurji wata sa’a kuwa cutar kan bayyana a kurarren lokaci wato gab da mutuwa.
A dalilin haka mutane da dama na dauke da cutar ba tare da sun sani ba sannan koda sun sani basu da masaniya game da yadda za su yi maganin ta.
Abinda ke kawo cutar Daji
1. Zukar taba Sigari.
2. Shan giya.
3. Yawan kiba a jiki.
4. Rashin motsa jiki
5. Shakar gurbataccen iska.
6. Kamuwa da wasu cututtuka kamar su Hepatities da kanjamau.
Alamun kamuwa da cutar
1. Rama
2. Jiri.
3. Kumburi ko kuma bullowar kurarraji a jiki musamman a nono.
4. Yin tarin da baya jin magani.
5. Zuban jini ta nono ko kuma ta dubura
6. Raunin da baya warkewa.
7. Rashin iya cin abinci