Sanata Binta Masi ta sha kaye a zaben kujerar sanata mai wakiltar Shiyyar Adamawa ta Tsakiya.
Binta Masi da ke wakilyar APC, ta sha kaye a hannun Ishaku Cliff na jam’iyyar PDP.
Binta ta samu kuri’u 16,219, shi kuwa Cliff ya samu kuri’u 43,117.
Binta ita kadai ce ‘yan majalisar dattawa daya tilo mace daga Arewa kakaf a zangon 2015 zuwa 2019. Ga shi kuma yanzu an kayar da ita.
Sai dai kuma an sake samun wata sabuwar sanata din daga jihar Adamawa, wannan kuma daga Adamawa ta Tsakiya. Aishatu Dahiru ta doke Mohammed Chubado da kuri’u 188,526. Shi kuma Chibadon ya samu 96, 530.
Aishatu daga APC shi kuma Chibadu daga PDP.