Dage zaben da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi da asubahin yau Asabar ya bar baya da kura sosai. Yayin da jiga-jigan ‘yan siyasa da sauran jama’a ke ta tofa albarkacin bakin su, PREMIUM TIMES HAUSA ta yi nazarin wasu matsaloli 10 da dage wannan zaben ya haifar, ko ma ya rigaya ya haifar.
TANTAMAR CEWA ZAI GUDANAR DA SAHIHIN ZABE
Shugaba Muhammadu Buharin ya sha fada sama da sau 50 cewa zai gudanar da zabe sahihi kuma karbabben da babu magudi a ciki. Sai dai kuma dage zaben da aka yi zai sa da dama, musamman ilahirin ‘yan adawa da masu sa-ido su fara tababar gaskiyar furucin da Buhari ya rika yi.
Na farko dai tun ana saura sati biyu zabe gwamnatin sa ta fara tankiya da masu sa-ido daga kasashen waje, saboda sun nuna katsalandan da Buhari ya yi ya dakatar da Cif Jojin Najeriya, Walter Onnoghen, wata daya kafin zabe.
Na biyu, a lokacin da Kadria Ahmed ta yi hira da Buhari kai-tsaye a gidan talbijin, makonni uku da suka gabata, ya bugi kirji ya ce bai yarda zai fadi zabe ba.
Sannan kuma ko a shekaranjiya, sai da ya sake jawabi, inda a ciki ya kara nanata cewa ba za a iya kayar da shi zabe ba.
Saboda haka dage zaben nan da aka yi, musamman kuma ganin yadda wasu matsalolin an fi jingina su a bangaren gwamnati, ya sa jama’a an tashi a yau ana tababar Buhari da ya ce zai gudanar da sahihin zabe.
JEFA ALAMOMIN TAMBAYA KAN INEC
Tuni jama’a da dama sun fara jefa alamomin tambaya a kan hukumar zabe, INEC. Ganin cewa an ba ta kudaden da ta ke bukata, kuma ta dade ta na shiri. Soke zabe ana saura sa’o’i biyar a tafi jefa kuri’a zai sa a rika tababar aikin hukumar duk da dai ta bayar da dalilan ta, ba kowa ne zai amince da su ba, musamman ma ‘yan adawa.
KAYAN AIKI DA MA’AIKATA
An yi wannan sanarwa bayan an rigaya an tura kayan aiki a yawancin jihohi har ma da kananan hukumomin kasar nan. Ya za a yi da wadanda aka rigaya aka tura. Ta ya za a iya tsare su ba tare da an sake kwashe su ko sake su ko lalata su ba?
INEC a nan ta haifar da dimbin asara, domin duk jami’in da aka tura sai an biya shi kudin aikin sa, kuma a mako mai zuwa sai an sake biyan sa wasu kudaden.
Wadanda za su fi jigata su ne matasa ‘yan bautar kasa da aka tura garuruwa daban-daban. An rika nuno da dama a cikin sun a barci a tashoshin mota ko cikin motoci ko kuma a tsakiyar hanya a cikin dare.
JAMI’AN TSARO
An rigaya an tura jami’an tsaro a jihohi da garuruwa da yankuma daban-daban. Kuma kowane daga inda aka kammala zabe sun gama aikin su kenan, sai fa wadanda za su yi aiki a wuraren tattara kuri’u kawai. Saboda haka babbar asara ce a sake maida su wuraren aikin su, bauan kwana hudu kuma a sake kwasar su a maida su.
AN KASSARA MATAFIYA GIDA SU YI ZABE
Da yawan mutane sun yi tafiya mai nisa daga garuruwan da suke harkoki ko aiki, sun tafi garuruwan su domin su yi zabe. An tsaida musu harkokin su, kuma an ja musu asarar kudaden tafiyar da su ka yi da kuma wanda za su koma, har ma da wanda za su sake komawa a mako mai zuwa. Wanda bai samu damar komawa ba kuwa, tilas ya ce an zalince shi, an tauye masa hakkin zaben wanda ya ke so.
DALIBAI DA AKA SALLAMA ZUWA GIDA DOMIN ZABE
Wannan dage zabe zai kara shafar karatun dalibai wanda aka ba hutun dan lokaci domin zuwa gida su yi zabe, ko kuma saboda za a yi amfani da wasu wurare domin aikin zabe. Akwai matsala dalibi ya koma gida, bayan kwana uku kuma a ce ya koma makaranta. Idan ya koma, bayan kwana uku kuma a ce ya sake komawa gida za a yi zabe.
MA’AIKATAN GWAMNATI DA NA KAMFANONI
Ma’aikatan gwamnati da suka tafi garuruwan su domin yin zabe, ba zai yiwu su zauna su shantake har sai wani makon bayan sun yi zabe sannan su koma ba. Haka kuma duk wanda ya koma garin da ya ke aiki a yanzu, to ba lallai bane ya kowa sake jefa kuri’a a mako mai zuwa.
Wadanda wannan abu zai shafa sosai sun hada har da kamfanonin jaridu na ‘online’, jarida, talbijin da kuma radiyo. Manyan kafafen yada labarai duk sun kashe kudade sun tura wakilan su garuruwa da dama domin tattaro musu wainar da za a toya tun daga ranar farar zabe har zuwa bayan bayyana sakamako.
Babu jaridar da za ta bar wakilin ta ya zauna can tsawon mako guda. Idan kuma ya koma wurin aikin sa, to fa tilas sai an sake maida shi a mako mai shigowa.
KASUWANCI DA SANA’O’I
Tun ranar Alhamis dama an yi sanarwar cewa an haka zirga-zirgar ababen hawa a yau Asabar saboda zabe. Kowane dn kasuwa ya sakankance ba zai fita ba. Da dama za su rasa cinikin yau kuma su rasa na wani satin mai zuwa.
Wadanda abin zai fi shafa su ne masu kayan gwari da danyun kaya irin kifi, nama da sauran abinci mai saurin lalacewa.
MASU SA-IDO DAGA KASASHEN WAJE
Akwai masu sa-ido daga kungiyoyi da hukumomi sama da 40 da kasashen waje. Yawan su ya tasar wa 700, idan aka yi la’akari da tawagar mutane 200 ta ECOWAS ita kadai. Cigaba da sake biyan kudin kwana a otal-otal da abinci har tsawon mako daya, wani jan aiki ne a gabn su, domin bajet din da suka yi wa kan su babu sati daya da aka kara a ciki.
MASU BUKUKUWA
Da yawa sun sa ranar bukukuwa a ranar Asabar mai zuwa, wanda wannan dage zaben zuwa wancan satin zai kawo wa cikas kenan. Tilas su ma sa sun dage bukukuwan na su, domin a ranar ababen hawa ba za su yi zirga-zirga ba.