Abin da ya sa Najeriya ta fi kowace jam’iyya Muhimmanci – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa Najeriya ta fi kowace jam’iyya muhimmanci, a kasar nan.

Buhari wanda shi ne dan takarar zaben 2019 na shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayyana wannan ra’ayin ne a yau Laraba yayin da ya ke jawabi wurin taron rattaba yarjejeniya ta karshe ta zaben 2019, a Babbar Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa a Abuja.

Buhari y ace wannan zabe mai zuwa ya na damuhimmaci kwarai da gaske ga kasar nan da kuma kafuwar dimokradiyyar kasar.

Ya ce jama’a da dama sun dora idanun su domin ganin cewa an gudanar da zabe sahihi kuma karbabbe, kuma duk da irin shirin da masu gudanar da zabe suka yi, ba za a rasa cimma kabubale ba.

Ya ce abu na biyu dangane da zaben shi ne wannan mai zuwa zai zo bayan na 2015 da aka gudanar, wanda kowa ya tabbatar da cewa sahihin zabe ne aka gudanar.

Shugaban ya kara da cewa abu na uku shi ne ganin yadda matasa suka yi ambaliyar shiga wannan zabe, saboda shrin ‘Not Too Young To Run da aka shigo da shi.

Akwai kuma tumbatsar yawan jam’iyyu da aka yi wannan zaben, wanda ba a taba samun yawan jam’iyyu kamar wannan zaben ba.

Daga nan sai ya yi kiran da kowa ya bada tasa gudummawa domin tabbatar da samun nasarar zaben, ya na mai cewa Nijeriya ta fi kowace jam’iyyar siyasa muhimmaci.

Buhari ya kara da cewa sai da ya tabbatar INEC ta samu dukkan kayann aikin da ta ke bukata. Ya kuma yi addu’ar Allah ya sa a gudanar da zabe lafiya.

Buhari ya gode wa wasu kungiyoyi na musamman Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Rainon Ingila.

Share.

game da Author