Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sha alwashin cewa idan aka zabe shi, to zai kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in kasar a ranar da ya fara aiki.
Ya yi wannan alwashin ne a taron bayar da lambobin yabo na Gwarzon Shekara da Silver Bird ya shirya a Legas.
Ya ce farkon abin da zai fara yi a ranar da aka rantsar da shi, shi ne nada ministocin sa, kuma a wannan ranar ce zai magance matsalolin yajin aikin lamaman jami’a.
Atiku ya ce ilmi a kasar nan ya yi tsaye cak wuri daya, tun bayan da aka fara yajin aiki, watanni hudu da suka gabata.
“Abin kunya ne a ce daliban jami’a na gida zaune na su karatu, har tsawon watanni hudu, an kasa shawo kan matsalar.”
Wazirin Adamawa ya ce idan aka zabe shi, ya yi alkawarin nunka kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa a fannin ilmi har zuwa nunki uku.
“A yanzu gwamnati na kashe kashi 7 bisa 100 na kasafin kudi a fannin ilmi. Amma ni idan aka zabe ni, to zan rika ware kashi 20 visa 100 na kasafin kudi ga fannin ilmi.” Inji Atiku.
Discussion about this post