A daina nuna wa masu dauke da cutar Kanjamau wariya a cikin mutane – Sani Aliyu

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau ta kasa (NACA) Sani Aliyu ya yi kira ga gwamnati data karfafa dokar hana nuna wa musu dauke da cutar wariya.

Aliyu ya yi wannan kira a shirye-shiryen da hukumar ke yi na ranar wayar da kan mutane game da illolin nunawa masu dauke da Kanjamau wariya da ake yi duk ranar daya ga watan Maris.

Ya ce karfafa dokar a kasar nan zai zama hanyar samar da kula wa mutanen dake bukata sannan zai zama hanyar dakile yaduwar cutar.

Dokar ya nuna cewa laifi ne a nuna wa mai dauke da wannan cutar wariya ta ko wace iri sannan laifi ne wuraren dake daukan mutane aiki su tursasa mutum sai ya yi gwajin cutar kanjamau kafin a bashi aiki.

Aliyu ya kuma ce kamata ya yi gwamnati ta wayar da kan mutane game da wannan dokar domin masu dauke da cutar su iya kare hakin su.

Jami’in UNAIDs Michel Sidibé a nashi tsokacin ya ce hana nuna wa masu dauke da kanjamau wariya hakki ne na kowa da kowa a fadin duniya.

Ya ce idan aka hada hannu gaba daya wajen hana nuna wa masu dauke da kanjamau wariya zai taimaka wajen hana yaduwar cutar a duniya.

Share.

game da Author