6-0: Manchester City ta babbake Chelsea

0

Kungiyar Manchester City ta lakada wa Chelsea kwallaye har 6:0, wadanda 4 a cikin kwallayen an ci su ne a cikin minti 25 da fara wasa.

Wannan ‘yar-gala-gala ko mari da tsinka riga da aka yi wa Chelsea ya taimaka wa City sake hawa ta farko a gasar PREMIER, inda ta sha gaban Liverpool.

Tun a minti na 4 Raheem Sterling ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea. Shi kuma dan wasa Sergio Aguero ya jefa kwallaye 3 shi kadai a minti na 13, 19 da kuma na 56.

Gundugan ya ci kwallo a minti na 25, shi kuma Sterling ya sake jefa cikin ta 6 a minti na 80.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci Sarri, mai horas da Chelsea ya rude kuma ya gigice saboda an kwarara masa kwallaye har hudu.

Yanzu dai daukar Kofin Premier za a ce ba a san maci tuwo ba tukunna, tsakanin Manchester City da kuma Liverpool.

Share.

game da Author