Idan ba a manta ba Radiyon BBC Hausa ta ruwaito labarin wani mazaunin kauyen Unguwan Gero dake karamar hukumar Kanaam Jihar Filato da wai ya saki matar sa a gaban mahaifinta saboda ta rantse sai ta sake zaben Buhari a Zabe mai zuwa.
Wannan Labari dai ashe tatsuniya ce babu gaskiya a ciki.
A binciken jaridar ‘Daily Trust’ ashe ma’aurantan masu suna Fatima da Abdullahi Yada’u suna zaman su lumui sumul babu tashin hankali.
Da yake yi wa Daily Trust bayanin abinda ya faru har wannan labarin karya ya karade gidajen Jaridun duniya Abdullahi ya ce “Wata rana Muna hiran siyasar kasar nan a wani wajen da mukan taru mu tattauna da yamma sai wani abokina Mai suna Maidankali yace zai yi kyawun gasket Idan da zamu saka labarin a yanar gizo ko Kuma Radiyo.
” Duk sauran wadanda muke tare dasu a wannan wuri Suka tashi Suka bar maganan a nan wurin.
Maidankali ya nemi ayi haka da ni sai naki amincewa na ce masa ba zan yi haka. Na yi banza dashi nayi tafiya ta.
Ashe ya garzaya tare da hadin baking wani abokina sa Mai suna Hamisu Suka he Suka Kira wakilin BBC Hausa inda daga nan shi Hamisu ya yi kamar shine Dan uwan Mata na da ya nemi yayi mini duka wai mahaifin su ya Hana bayan na saki matata. Shi Kuma Maidankali ya tsaya a matsayin na.
Yada’u ya ce rundunar ‘yan sandan garinsu na nan na neman Maidankali da Hamisu bisa wannan rashin hankali da Suka yi.
Ita kuwa mai dakin Yada’u, Fatima ta ce wadannan mutane biyu sun yi haka ne domin su ci wa auren ta mutunci ganin cewa tana zaman lafiya da mijinta.
” Da farko dai suna na ba Hafsat ba ne, suna na Fatima ne. Yadda na San abinda wadannan mutane suka yi wa mijina shine kawai an wayi gari ne naga mutane suna ta tururuwa zuwa gidan mu wai sun zo yi mani Allah ya kiyaye da jajanta min wai mijina ya sake ni.
” Ina so in sanar wa duniya cewa bamu taba samun sabani da mijina ba sannan maganganun wai ya sake ni saboda zaben Buhari ko Atiku bai taba taso was tsakani na da mijina ba. Ko yatsa bai taba nuna min ba. Sharri ce kawai wadannan mutane suka shirya don su ci Mana mutunci.
Idan ba a mantaba a ranar 24 ga watan Janairu ne PREMIUM TIMES ta wallafa labarin da BBC ta ruwaito na yadda wani magidanci a karamar hukumar Kanaam jihar Filato ya saki matarsa a dalilin rikicin da ya kaure a tsakanin su saboda matarsa ta rantse sai ta zabi Buhari.
Maigidan na ta ya ce matarsa ta tabbatar masa cewa ita fa Atiku za ta zaba a Faburairu.
Daga nan ne fa suka fara cacan baki a tsakanin su, shiko gogan naka sai ya mike tsaye ya falla mata mari. Ita kuma ta rika ce masa wallahi sai ta zabi Buhari.
Ashe dai wannan Labari bai faru ba duk da muryoyin da suka shaida wa BBC cewa sune abin ya faru da.