Sakamakon binciken sanin yawan likitocin da Najeriya ke da su da PREMIUM TIMES ta gudanar ya tabbata cewa fannin kiwon lafiyar kasar nan na fama da karancin likitoci.
Wakiliyar PREMIUM TIMES da ta gudanar da wannan buncike bisa rahoton hukumar yi wa kwararrun likitoci rajista na kasa (MDCN) ta gano cewa yawan likitocin da suka yi rajista da ita a yanzu haka sun kai 42,845.
Rahoton ya nuna cewa a duk shekara likita daya a Najeriya na kula da marasa lafiya 4,850 wanda hakan ya saba wa dokar aiyukkan likitoci da kungiyar kiwon lafiya ta duniya.
Bisa ga wannan dokar kamata ya yi a shekara likita ya kula da marasa lafiya 600 domin samar da kiwon lafiya mai nagarta.
A nashi tsokacin shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA) Francis Faduyile yace hakan na da nasaba ne da rashin samun ingantattun kayan aiki da rashin biyan likitoci albashi mai tsoka da dai sauran su da ake fama da su a fannin kiwon lafiyar kasar nan.
Faduyile yace a dalilin haka kwararrun likitocin dake kasar nan ke tattara nasu-i-nasu suke ficewa daga kasar nan domin zuwa Kasashen da za a daraja aikin su da biyan su kudade masu tsoka.
Binciken ya kara nuna cewa rashin daraja likitoci a kasar nan zai iya yi wa burin samar da kiwon lafiya mai nagarta wa kowa a kasar kafar angulu.
A yanzu haka gwamnatin kasar nan ta tsara wasu matakan da za su taimaka wajen cimma wannan buri nata amma duk da haka bata da masaniyya game da adadin yawan likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiyar dake ficewa daga kasar.
Sai da duk da wadannan matsaloli ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce karancin likitocin da ake fama da su a kasar nan bai taka kara ya karya ba.
Adewole ya ce babbar matsalar fannin kiwon lafiyar kasar nan shine rashin samun ma’aikata a inda aka fi bukatan su.
” Misali a yankin karkara babu ma’aikatan kiwon lafiya a inda a irin wadannan yankuna ne aka fi bukatan su. A birane kuwa ma’aikatan kiwon lafiya sun yi yawa har akan rasa inda za a iya yi da su.
Adewole ya ce kawar da wannan matsalar zai taimaka wajen kawo wa fannin kiwon lafiyar kasar nan cigaban da ake bukata matuka.
Discussion about this post