Shugaban rundunar soji na barikin Rukuba dake Jos jihar Filato Ikechukwu Stephen ya bayyana cewa wani soja ya rasu a dalilin kamuwa da zazzabin Lassa.
Stephen ya tabbatar da haka ne wa PREMIUM TIMES ranar Alhamis a garin Jos yana mai cewa sojan ya rasu ne a asibitin Bingham dake Jankwano a Jos.
Ya bayyana cewa sojan ya fara rashin lafiya ne bayan ya dawo daga jana’izar mahaifinsa a jihar Kogi.
” Daga nan sai aka kwantar da shi a asibitin sojoji dake barikin. A haka ne fa da jikin nasa ya ki lafiya sai aka maida shi asibitin Bingham. A wannan asibiti ne ya cika.
Stephen ya ce sojan ya rasu ranar 15 ga wantan Janairu sannan ya yi jinyar kwanaki hudu ne kawai.
Discussion about this post