Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Filato Kunde Deyin ya bayyana cewa zazzabin lasa ya yi ajalin mutane hudu a jihar.
Deyin ya fadi haka ne a yau Alhamis mako daya da rundunar sojin Najeriya ta sanar da mutuwar wani soja a dalilin kamuwa da cutar.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne wani soja dake aiki da barikin soji dake Rukuba a Jos ya rasu a dalilin kamuwa da cutar bayan ya dawo daga jana’izar mahaifinsa a jihar Kogi.
Rundunar ta ce sojan ya yi jinyar tsawon kawanki hudu kafin ya rasu a asibitin Bingham dake garin Jos.
A bayanan da ya yi Deyin ya ce sun gano cutar ne bayan gwada mutane 25 da ake zaton sun kamuwa da cutar inda sakamakon gwajin ya nuna cewa mutane 16 na dauke da cutar.
Ya ce wadannan mutane 16 da ke dauke da cutar na samun kula a asibitin Bingham da asibitin koyarwa na jami’ar Jos.
” Mun kuma gano cewa wadannan mutane 16 din dake dauke da cutar mazaunan kananan hukumomin Jos ta Arewa ce, Jos ta Kudu, Bassa, Riyom da Shandam.
A karshe Deyin yace gwamnati ta dauki matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar.
Wannan sanarwa da Deyin ya yi a yau ya zo ne bayan kwanaki biyu da hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa(NCDC) ta sanar cewa cutar ta sake bullowa a kasar nan.