ZARGIN KWARTANCI: Miji ya kashe matar sa da ‘ya’yan sa biyu

0

Wani mutum mai suna Uwaila, ya bindige matar sa da kuma ‘yan’yan sa biyu har lahira, saboda zargin kwartanci.

Uwaila mai shekaru 35 a duniya, ya aikata kisan ne a garin Ovbiogie cikinn karamr hukumar Ovia ta Arewa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Hakeem Odumosun, ya kai ziyarar gani da ido a inda abin ya faru, kuma ya tabbatar da cewa da zarar ann kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban hukuma.

An ce wanda ya aikata kisan ya harde gardandami da tankiya tare da matar da ‘ya’yan, inda ganin abin ya yi tsamari, su kuma suka gudu suka shige wani daki suka kulle kan su a ciki.

Uwaila ya fusata, inda ya rungumo bindiga ya rika darzaza harbi ta cikin murfin kofar dakin.

Da ya ke bayyana yadda abin ya faru, wanda ya yi kisan ya bayyana cewa matar sa ta yi zargin wai ya na da wasu ‘yan mata da ya ke nema, ita kuma ta yi barazanar ramawa ta hanyar rika neman wasu mazajen.

Ya ce ya fizgi mota ya fice daga gidan, amma da ya dawo, sai ya taras matar ta kulle kan ta cikin daki tare da ‘ya’yan sa biyu a cikin daki.

Wanda ake zargin ya ce ya yi harbi ta jikin kyauren kofar dakin, inda harsashe ya samu kawunan matar da ‘ya’yan na sa.

Share.

game da Author