Jiya Laraba da dare ne, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi hira ta musamman da Kadaria Ahmed. An nuna hirar kai-tsaye a gidan talbijin na NTA na Kasa, kamar yadda aka nuna wadda shugaba Muhammadu Buharin ya yi tare da ita cikin makonni biyu da suka gaba ta.
Dukkan ‘yan takarar biyu dai sun yi tattaunawar ce tare da mataimakan takarar ta su. Buhari ya je tare da Yemi Osinbajo, shi kuma Atiku Abubakar ya je tare da Peter Obi.
PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo muku yadda ta kasance a babban dakin taro na Sheraton Hotel jiya da dare, domin ku samu abin karin kumallo yau da safe.
BATUN MAKOMAR WADANDA SUKA WAWURI KUDADE
Atiku Abubakar ya ce idan ya ci zabe zai iya yi musu afuwa matsawar za su maido dukkan abin da suka wawura.
Atiku ya ce zai shata layi, ya yi shelar yin afuwa ga dukkan wanda ya wawuri kudade, kuma zai bayar da wa’adi cewa duk wanda ya maido, to ba za a gurfanar da shi kotu har a hukunta shi ba.
Ya ce to idan wa’adin ya cika, sai ya daura sirdin sabon yaki da cin hanci da rashawa gadan-gadan, na ba sani ba sabo.
Kadria ta ce ba ya ganin yin hakan zai zama matsala gare shi, domin shi ma an zarge shi a lokacin da ya yi mulki na mataimakin shugaban kasa?
Atiku ya ce ai idan ya ce zai ci gaba da shari’ar su, to za a yi ta bata shekara da shekaru ne kawai, ba tare da kotu ta karbo kudaden da aka waura ba.
Ya buga misali cewa gwamnatin baya ta shigo da tsarin da ya ce zai zawo da shi, kuma sai da aka maido sama da dala bilyan 4.
PETER OBI: BABU SAURAN BARAGURBI A PDP, DUK SUN KOMA APC
Dantakarar Mataimakin Shugaban Kasa Peter Obi, ya ce ai yanzu jam’iyyar PDP wankakka ce sumul kuma kanshin turare ta ke yi.
Obi ya ce marasa gaskiyar cikin jam’iyyar duk sun koma bayan Buhari kuma su ne ke tallata sake zaben sa. Ya ce su na tsoron bincike ne shi ya sa duk suka sulale suka koma APC.
Ya kuma kara yin bayanin cewa yaki da cin hanci da Buhari ke yi duk tasuniya cevkawai, domin ‘yan adawa ake wa bi-ta-da-kulli, ana kyale makusantan Buhari ko wadanda suka ci suka take cikin su, yanzu kuma su ka koma bayan Buhari.
IDAN NA FADI ZABE ZAN AMINCE, AMMA IDAN BA A YI MAGUDI BA
Atiku Abubakar ya amsa tambayar da aka yi masa ta karshe a kan ko zai amince da sakamakon zabe idan ya fadi?
Ya ce ai ya sha faduwa zabe a baya ba sau daya ba. Kuma faduwa zabe ba abin kunya ba ne. don haka idan ya fadi zai yarda da kaddara, amma fa idan kowa ya tabbatar da cewa sahihin zabe kuma ingantacce wanda babu magudi aka gudanar.
Shi kuwa Buhari da aka yi masa wannan tambayar a baya, maimakon ya amsa kai tsaye, sai ya ce ai zabukan baya ma da ya fadi, duk kayar da shi aka yi. Don haka bai ga yadda zai fadi zabe ba.
YADDA ZAI MAGANCE RIKICINN MAKIYAYA DA MANOMA
Atiku Abubakar ya ce za a duba dokar hana kiwon da wasu jihohi suka kakaba domin yin nazarin abin da dokar kasa ta tanadar dangane da haka.
Ya ce idan ya cei zabe, gwamnatin sa za ta tashi tsaye haikan wajen ingantawa da samar da ilmantarwa ga makiyaya.
Atiku ya ce idan aka kara wayar wa makiyaya kai sosai, to tsarin da za shigo musu da shi zai zama mai amfani gare su da kuma gwamnati baki daya.
Ya ce yin hakan za a rika samun kudaden shiga sosai su kuma makiyayan za su rika samun madara da nama saosai.
Jihohin Taraba da Benuwai da Ekiti ne suka kakaba dokar hana kiwo.
Atiku wanda an yi ikirarin ya na da makeken garken shanu, ya ce idan ya ci zabe zai yi kokarin kawo tsarin da zai takaita zirga-zirgar makiyaya ta yadda za su yi kiwo a cikin sauki.
Ya kara da cewa babbar hanyar da za a dakile rikicin ita ce fadada tsarin ilmantar da Fulani, ta yadda shi kan sa yawace-yawacen zai rika fita daga ran su ko daga al’adar su.
BOKO HARAM: ZAI KORI KWAMANDAN DA YA BARI ANA KASHE SOJOJIN A KARKASHIN SA
Atiku Abubakar ya ce zai hukunta dukkan wani kwamandan da ya bari ana karkashe sojoji kuma ana kwace makamai a karkashin sa.
Ya ce kafin sannan kuma sai ya tabbatar da ya gano babbar matsalar sojojin. Idan ma rashin ingantattun makamai ne, to zai gaggauta samar da su kuma wadatattau.
Sannan kuma zai samar wa sojoji horo mai inganci matuka, kuma za a kara kula da jin dadin su da inganta rayuwar su matuka, yadda ba za su rika jikarar komai ba, kuma za a kara musu kwarin guiwar yin azamar magance kalubalen da ke gaban su.
Ya ce amma ba zai lamunci duk wani kwamandan da zai yi sake har Boko Haram su rika karkashe sojojin da aka ba shi hakkin jagorantar su zuwa yaki ba, kuma aka rika karbe musu makamai a yaki da Boko Haram.
RIKICIN ‘YAN SHI’A
Atiku Abubakar ya soki lamirin yadda sojoji suka biye wa ‘yan Shi’a har aka yi mummunan kashe-kashen daruruwan fararen hula a Zaria da Kaduna.
Ya ce bai ga dalilin da zai sa a saka sojoji wajen dakile zanga-zangar ‘yan Shi’a ba a 2015.
Atiku ya ce abin da kowa ya sani shi ne, idan ma sun karya doka, to ‘yan sanda za a tura musu, amma ba sojoji ne za su je su yi ta bude musu wuta ba.
An tambaye shi me ya kamata sojoji su yi a lokacin da ‘yan Shi’a suka tare hanya, suka hana su wucewa?
Sai Atiku ya ce ai babu ruwan sojoji da ‘yan Shi’a. Kamata ya yi a kai musu ‘yan sanda a lokacin.
A Zari’a dai sojoji sun kashe mutane 347, wadanda gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe su.
Su kuma ‘yan Shi’a sun ce an kashe musu mutane sun kai 1,000, cikin su har da ‘ya’yan Sheikh El-Zakzaky hudu da Sheikh Turi. An kuma harbi malamin da matar sa Zeenat, kuma su na tsare tun a ranar 15 Ga Disamba, 2015 har yau.
Discussion about this post