Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, A tiku Abubakar, ya kara jaddada matsayar sa cewa tabbar idan ya ci zabe, sai ya saida kamfanin mai na NNPC, ko da kuwa za a kashe shi.
Ya kuma yi alkawarin rubanya tattalin arzikin Najeriya.
Kafar yada labarai ta Reuters ta ruwaito Atiku, wanda hamshakin dan kasuwa ne, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa na mulkin Olusegun Obasanjo, tsakanin 1999 zuwa2007 ya na cewa:
“Idan na zama shugaban kasa zan rubanya tattalin arzikin Najeriya ta yadda daga nan zuwa 2025 za a samu karin dala bilyan 900 ga tattalin arzikin Najeriya.”
“Zan saida kamfanin NNPC ko da kuwa za a kashe ni ne. domin ta haka ne za mu iya karfafa tattalin arzikin kasar nan. Ba kuma a kan NNPC zan tsaya ba, zan kafa kwamitin mashawarta da za su bada shawarar duk wani abu da ya dace a saida domin tattalin arzikin kasar nan ya karfafa.”