Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya shaida cewa idan ya ci zabe ba zai yi irin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke yi ba ya na karya dokoki da kuma sa kafa ya na tattake su.
Attiku ya ce zai bi doka da oda kuma zai yi komai a bisa yadda dokar kasa ta gindaye, ba kuma zai tauye ko danne hakkin kowa ba.
Atiku wanda ya nuna cewa abin da Buhari ke yi wajen tattake dokokin kasa barazana ce ga dimokradiyya, ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke gabatar da bayani ne dangane da yadda Buhari ya dakatar da Cif Jojin Najeriya, Walter Onnoghen, ba tare da ya tuntubi Majalisar Dattawa kamar yadda dokar kasa ta gindaya ba.
Ya yi jawabin ne a wurin taron cikar Lagos Island Club shekaru 75, jiya Laraba, a Legas.
Atiku ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye su kare dimokradiyya, domin Buhari na kokarin karya ta ta hanyar tattake dokoki da yin biris da abin da kundin tsarin mulkin kasa ya gindaya.
Wazirin na Adamawa, kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ya ce duk da Buhari ya yi kokarin ganin ya tsige shugaban majalisar dattawa, amma bai samu nasara ba, maimakon ya nabba’a, ya hakura, sai da ya sake kitsa wani tuggun na karya bangaren shari’a na kasar nan, wanda shi ma sashe ne mai zaman kan sa.
An cire Onnoghen watanni kadan bayan yunkurin da aka yi na mamaye Majalisar Dattawa, wanda masu adawa suka ce an yi ne da nufin cire Shugaban Majalisa, Bukola Saraki.
An cire shugaban DSS na lokacin, Lawan Daura, saboda tura jami’an sa da ya yi suka mamaye majalisa, ba tare da sanin gwamnatin tarayya ba.