Dan takarar gwamnan jihar Kaduna, Hon Isah Ashiru ya tabbatar wa mutanen Kaduna cewa idan har Allah ya bashi sa’an darewa kujerar mulkin Jihar Kaduna, zai tabbata ya dawo wa Kaduna da martabarta a idanun mutanen jihar da kasa baki daya.
Ya ce gwamnati mai ci bata taka rawar gani ba wajen kwararo wa mutanen jihar Kaduna romon dimokradiyya sai dai dandana musu azabar gaske ta hanyar raba su ayyukan su da hanyoyin samun wadatar rayuwa da tayi.
Isa Ya kara da cewa gwamnatin sa za ta zamo gwamnati ce mai gaskiya da rikon amana sannan mai kishin talaka.
” Idan Allah ya bamu sa’ar darewa wannan kujera na mulkin jihar Kaduna, zamu jawo kowa dan jihar a taru waje daya a yi aiki tare. Sannan zamu tabbata talaka ya shaida cewa lallai gwamnati mai adalci da kishin sa ne ke mulki a jihar.
” Bayan nan zamu tabbata mun saita jihar a kan tafarkin gaskiya da rikon amana sannan kuma mu rika yi wa mutane ambaliyar ababen more rayuwa ta hanyar inganta asibitocin mu a birane da kauyuka, tallafa wa talaka da sana’o’i da kuma tabbatar da ganin an samu daidai tuwa a tsakanin mutanen jihar da zaman lafiya mai dorewa a ko-ina- a fadin jihar.
Wadannan sune ire-iren kalaman da Isa Ashiru ya rika yi a karamar hukumar Lere inda ya ziyarci fadar mai martaba Lamidon Lere, Abubakar II da wasu daga cikin garuruwan da ya ziyarta a kamfen din sa a makon da ya gabata.
A tawagar Isah akwai tsohon gwamna Ramalan Yero, Sanata Suleiman Hunkuyi da jiga-jigan ‘yan jam’iyyar PDP na jihar Kaduna