Insha Allah duk mahalukin da yake Kano sai ya ga ko kuma ji labarin irin ayyukan da kungiyar ‘The Youths-4-Change Network’ take yi. Babu shakka wannan kungiya tana neman zama ruwan dare a cikin garin Kano akan rajin da take yi na gina sabuwar Najeriya da gudunmuwar bulo, yashi, siminti da katako daga matasan Najeriya.
Duk kungiya tana iya samun nasara idan an kafata da kyakykyawar niya, hakazalika tana iya rushewa idan aka kafata da son zuciya da kwadayin neman arziki kawai. Arziki Allah ne yake bayar da shi ga wanda yaso a sanda yaso don haka idan yaso zai baka a kodayaushe. Manufofin kungiya na arziki su zasu baku nasara da arziki idan Allah yaso.
Wannan kungiya da kake ganinta, ya kai mai karatu, ta fara ne kamar da wasa amma cikin taimakon Allah ta fara girma a ciki da wajen Kano. A kashin gaskiya ba zan iya cewa ga lokacin da ayyukanta suka tumbatsa ba amma kuma ba zan yi mamaki ba saboda Allah yana taimakon wadanda suka tsarkake zuciyar su kuma suka jajirce akan abun da suke yi ko min qanqantarsa.
Mun fara yawon fadakarwa ne tun daga gidajenmu har zuwa jiharmu da wajenta. Tsarki ya tabbata ga Allah, a kokarin gina sabuwar Najeriya, wannan kungiya ta saka kafarta a waje daban-daban, gidajen radiyo, TV da jaridu, manyan wuraren taro da sauransu.
Cikin ikon Allah, mun samu shuhura ne tun daga ayyukanmu na cigaban matasa kafin mu fara yin abun da muka yi masa lakabi da ‘Kano Preelection Youth Mobilization for Political Change’ wanda hotuna suke yawo a jikin ababan hawa da alluna a gefen titi da kuma riguna da sauransu. Wannan aiki yana da qudirin wayar da kan matasa akan zabe da tasirinsa ga rayuwar talaka.
Sannan akwai gagarimin makon lafiya (Medical outreach) da zamu yi a ranar 26 ga watan da muke ciki insha Allah. wannan makon lafiyar zai gwada masu cutar hawan jini, ciwon hanta, da siga ya kuma basu magani kyauta idan Allah yaso. Wadannan ayyuka zasu gudana ne kafin zabe, muna da manyan ayyuka (Projects) bayan zabe saboda duniya ta san cewa wannan kungiya a shirye take ta kawo cigaba a cikin matasa ko da siyasa ko babu ita.
Wannan kungiya tana nan tana yawo a bayan adaidaita sahu, motocin gida da na haya har da yaya babba (Tipper da trailer). Watarana ma idan Allah yaso har a jikin jirgin sama za a ga hotunanta saboda a dade ana yi sai gaskiya.
Kokarin da muke yi shine, fadakarwarmu ta zama ruwan dare a wajen matasa ta yadda ko bayan mun mutu wasu zasu cigaba shiyasa ni Comrade M.K Soron dinki da sakataren wannan kungiya Comrade Idris I Garin Babba duk gidan radio ko TV din da bamu shiga ba a Kano sunansa soriye. Kuma muna kan hanyar zuwa ko ina mu fadakar don samun sabuwar Najeriya.
Allah yasa mu ga Alheri.
Discussion about this post