ZABEN 2019: INEC za ta gana da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) a ranar Juma’a

0

Ganin cewa gwamnatin tarayya ta kasa sasantawa tsakanin ta da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa, wato ASUU, ga shi kuma zaben 2019 ya tunkaro, hakan ya sa Hukumar Zabe ta Kasa, INEC tunanin zaman tattaunawa da kungiyar ta malaman na jami’a.

Shugaban Kungiyar ASUU, Biodun Ogunbiyi, ya tabbatar wa da PREMIUM TIMES cewa tabbas za su yi zaman da jami’an INEC a ranar Juma’a, 4 Ga Janairu, 2019.

Zaman inji shi zai karkata ne a yadda malaman jami’o’i za su taimaka wa INEC a zaben 2019.

Ya kara da cewa za a gudanar da taron ne a Abuja.

Tun a ranar 4 Ga Nuqamba, 2018 ne malaman suka shiga yajin aiki, wanda hakan ya jefa INEC a cikin damuwar da ta ce yajin aikin ka iya shafar aikin zaben 2019.

Sai dai kuma Kungiyar Manyan Malaman Jami’a ta Kasa, wato SSANU ita kuma ta ce yajin aikin ba zai shafi aikin gudanar da zaben 2019 ba, domin kowane zaman kan sa ya ke yi.

Babban Jami’in INEC Festus Okoye, ya bayyana cewa Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu na da yakinin cewa tattaunawar da INEC za ta yi da ASUU za ta yi tasiri sosai kuma za a samu nasarar cimma matsaya da kuma mafiyar yadda za su shigo cikin aikin gudanar da zaben 2019 ba tare da tangarda ba.

Share.

game da Author