Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya zargi INEC da kokarin sake dawo da amfani da tsohon tsari na amfani da sunayen masu kada kuri’a a cikin fam, maimakon na na’urar tantance masu jefa kuri’a, wato ‘Smart Card Reader’ a zaben 2019.
Wannan ne ya sa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC maida masa martani tare da musanta zargin da ya yi, ta na mai cewa ba gaskiya ba ne, kuma ba haka ba ne.
Cikin makonnin baya ne INEC ta bada sanarwar cewa ta kara jaddada matsayar cewa ba za ta yi amfani da tsarin ba, domin a gyara kura-kuran zabukan baya.
Sai dai kuma a cikin wani bayani da kakakin yada labarai na Atiku, Paul Ibe ya fitar jiya, ya zargi INEC da kokarin sake dawo da tsarin ya na mai cewa INEC ta karya alkawarin da ta dauka cikinn 2018 cewa ba za ta yi amfani da tsarin ba.
Ibe ya ce INEC ta dawo ta ce za ta yi amfani da shi.
Amma babban jami’in INEC, Oluwole Osaze-Uzzi ya ce karya ne ba gaskiya ba ne, kuma ya kalubalanci Atiku da ya nuna inda INEC ta bayyana zargin da ya yi mata.
Ya ce shi dai abin da ya sani ne cewa INEC za ta yi amfani da na’urar tantance masu zabe a 2019 kawai, amma bai san inda kakakin yada labarai na Atiku ya kwakulo zargin da ya ke yi, wanda ba gaskiya ba ne.
Discussion about this post