Kungiyar magabatan gabilar Ibo, wato Ohaneze Ndigbo ta karyata rade-radin da ke ta yadawa wai yankin Ibo ta amince da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar da zata zaba a watan Faburairu.
Sakataren kungiyar Chuks Ibegbu a shimfidaddiyar sako da ya fitar a madadin kungiyar ya bayyana cewa mutane su daina yadawa wai yankin kabilar Ibo ta tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar da za ta zaba a zabe mai zuwa.
” Ba dadidai bane a rika yadawa wai ‘yan kabilar Ibo sun tsaida Atiku a matsayin dan takarar shuagaban kasa da za su zaba a zabe mai zuwa. Taron da wasu ‘yan kabilar suka yi a garin Enugu taro ne na abokanan Atiku ba jam’in kabilar Ibo ba.
” Nan da ‘yan kwanaki kadan za mu bayyana dan takaran da za muyi a zabe mai zuwa. zamu gudanar da taron kungiyar sannan a nan za mu fitar da matsaya daya game da hakan.
” Mu a yankin Kudu Maso Gabas, za mu zabi mutumin da ke da muradin ci gaban Najeriya. Wannan shinr zamu karkata a kai wajen yanke shawarar wanda zamu marawa baya a zaben shugaban kasa mai zuwa.