ZABE: Yajin aiki ba zai hana malaman jami’a taya INEC gudanar da zabe ba – ASUU

0

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa, ASUU ta amince ta kyale mambobin su gudanar da aikin zaben 2019 tare da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).

Shugaban ASUU na Kasa baki daya, Biodun Ogunyemi ya bayyana wa manema labarai haka, bayan ganawar sa da shugabannin INEC.

Ya ce ASUU ba za ta hana hana malaman jami’o’I shiga aikin zaben 2019 a matsayin su na ma’aikatan wucin-gadi na INEC, domin gudanar da aikin zaben na cikin bangaren ayyukan sadaukarwa ga al’umma.

Ya ce dangantakar malaman jami’a da INEC ta samo asali ne tun daga hawan tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega.

Don haka ba za su bari wannan dangantaka da samu cikas ba don kawai ana yajin aiki.

Shi ma Shugaban Hukumar Zabe, INEC, Farfasa Mahmood Yakubu, ya nuna jin dadi da farin cikin sa dangane da amincewar da malaman jami’a suka yi cewa za su taimaka a yi aikin zabe tare da su.

Yakubu ya ce don haka ya na tabbatar wa ‘yan Najeriya da ma duniya baki daya cewa zaben 2019 na nan daram ba tare da tunanin samun wata tangarda ko tsaiko ba.

A KAN AMINA ZAKARI

Da aka tambaye shi batun Amina Zakari, Yakubu ya ce ba ta da wata alaka ta jini da Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce ita ‘yar asalin jihar Jigawa ce, shi kuma Buhari dan jihar Katsina.

Kafin nan dama sai da Fadar Shugaban Kasa ta maida wa PDP martanin cewa Amina Zakari ba ta da wata alaka ta jini da shugaba Buhari.

Share.

game da Author