ZABE: Masu sa-ido daga Kungiyar Tarayyar Turai su 40 sun dira Najeriya

0

Kwanaki 19 suka rage a jefa kuri’ar zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa, amma tuni har masu sa-ido daga Kungiyar Tarayyar Turai (EU) su 40 suka dira cikin Najeriya.

Jagoran tawagar mai suna David Dahmen, wanda shi ne zai sa ido a jihohin Oyo da Osun, ya shaida wa manema labarai haka a lokacin da ya kai ziyara ga kwamishinan zabe na tarayya, na jihar Oyo, Mutiu Agboke.

Dahmen ya ce ya je Ibadan ne domin gane wa idon sa yadda jihar ta ke, ya je an karkasa masu sa-ido din zuwa gida 20 domin sa-ido kan yadda za a gudanar da zabe a fadin kasar nan.

Ya ce shi da Mukalay Banze tare kuma da mataimakan su, wato Sony Odiongenyi ne za su sa-ido a Oyo da Osun.

Ya kara da cewa kwamishinan zabe na jihar Oyo ya yi musu irin bayanin irin kwakkwaran shirin da INEC ta yi domin zaben mai zuwa.
Dahmen yay i fatan za a gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali ba tare da magudi ba.

Share.

game da Author