ZABE: INEC ta yi kira a fito da sabon tsarin matakan tsaro

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta yi kira da a samar da sabon tsarin matakan tsaro a lokacin zabukan 2019 masu zuwa.

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ne ya yi wannan kiran, kwanaki 37 kafin zabe.

Ya yi wannan kira a lokacin da ya ke ganawa da jami’an tsaro na bangarori da dama a ci gaba da ganawa da ya kan yi da su a duk bayan watanni uku.

Ya kuma karfafa cewa ‘yan sanda su ne a sahun gaba wajen aiwatar da tsaro a lokutan zabe, sauran hukumomin tsaro kuma za su agaza musu ne.

Yakubu ya ce sun dauki darussa da dama a lokacin zabukan cike gurabu da sauran zabukan da aka gudanar tun bayan zaben 2015.

Dalili kenan ya ce akwai matukar bukatar fito da sabon tsarin samar da matakan tsaro yayin zabe.

Ya ce ya na so a yi komai a cikin tsarin da dokar kasa ta shimfida. Daga nan sai ya ce za a yi aki da sojoji ne wajen kai-da-kawon raba kayan zabe da kuma kwasowa daga inda aka yi zabe, sai kuma wajen kare lafiyar jami’an zabe kawai.

Share.

game da Author