ZABE: INEC na bukatar ma’aikata 15, 545 a Kwara, miliyan 1.2 a Najeriya -Yakubu

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta ce za ta tura ma’aikatan gudanar da zabe har 15, 545 a jihar Kwara domin gudanar da zaben 2019.

Kwamishinan Zabe na Tarayya da ke Jihar Kwara, Garba Attahiru Madami ne ya bayyana haka a Ilorin babban birnin jihar.

Ya ce ana bukatar ma’aikatan wucin-gadi 13, 199 da za su yi aikin gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya.

Sauran sun hada da jami’an zaben na dindindin.

Sannan kuma ya ce za a tura masu bautar kasa, wato NYSC har 7, 567 domin gudanar da zaben.

A wani jikon kuma, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa INEC ta na bukatar akalla jami’an gudanar da zabe da jami’an tsaro a kalla milyan 1.2 domin gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan.

Yakubu ya bayyana hakan ne a Kano, inda ya jaddada cewa INEC na bukatar akalla jami’an tsaro 360 da za su kula da rumfunan zabe a lokacin da ake gudanar da zabuka a ko’ina cikin kasar nan.

Shugaban na INEC ya yi wannan bayani ne ta bakin Sa’ad Idris, Shugaban Cibiyar Zabe ta Kasa da ya wakilce shi.

An shirya taron ne a Kano domin sanin makamar aiki lokacin zabe ga jami’an tsaro.

Tare da hadin guiwar Cibiyar Tallafa wa Zabuka ta Kungiyar Tarayya Turai aka shirya taron.

Kasancewa Najeriya na da masu jefa kuri’a har milyan 84, Yakubu ya ce Najeriya ce ta biyu a yawan masu jefa kuri’a a kasar da ake dimokradiiya a duniya.

Yakubu ya hori jami’an tsaro su yi aiki tsakanin su da Allah kamar yadda doka ta tanadar domin a tabbar da samun ingantacce, sahihi kuma karbabbe.

Share.

game da Author