Gwamnoni 36 na kasar nan na ganawar sirri tare da Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, Babagana Monguno.
Ana tattaunawar ce a yau Talata a Abuja.
An fara ganawar ce tun da karfe 12 na rana a Sakateriyar Kungiyar Gwamnaonin Najeriya da ke cikin Maitama, Abuja.
Wata majiya da ke da kusanci da kungiyar ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Moguno ne ya kira taron domin ya sanar wa gwamnoni irin shiri da kuma tsare-tsaren da aka yi dangane da zaben 2019 da za a fara gudanarwa daga ranar 16 Ga Fabrairu da kuma ranar 2 Ga Maris.