Tsohon Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Rainon Ingila, Emeka Anyaoku, ya bayyana cewa duniya kaf ta zura wa Najeriya ido domin tabbatar da ganin cewa an gunadar da sahinin zabe a ranakun 16 Ga Fabrairu da kuma 2 Ga Maris.
Anyaoku ya shawarci gwamnatin tarayya cewa akwai babban nauyi a kan ta na tabbatar da ganin an yi zabe sahihin Zabe ba tare da an murdiya ko magudi ko kwange ba.
Kuma ya yi fatan ba za a yi sake rikici ya barke a lokacin zabe da kuma bayan gdanar da zaben ba.
Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke jawabi wajen kaddamar da sabon tambarin Jaridar Tribune.
Anyaoku ya hori INEC da sauran hukumomin tsaron kasar nan cewa su sani duniya kaf ta zura musu ido ana jiran a ga sun gudanar da sahihin zabe ba tare da tashin hankali da murdiya ko magudi ba.