ZABE: Amurka ta nuna damuwa kan jami’an tsaron Najeriya

0

Amurka ta bayyana bamuwa da tababar ta kan yadda jami’an tsaron Najeriya za su yi aiki a lokacin zabe ba tare da yin katsalandan a zaben ba.

Za a fara gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya da sanatoci a ranar 16 Ga Faburairu.

Wakilin Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, David Young ne ya bayyana haka a wani taron ganawa da jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC a jiya Laraba, a Abuja.

An gudanar da tarin ganawar ce a hedikwatar INEC da ke Abuja.

“Mu na da damuwa sosai dangane da yadda za a iya samun nasara cewa jami’an tsaro ba su hana masu zabe zaben wanda suke so ba, kuma ba su yi wani abu da zai takura wa masu sa’ido da kungiyoyin buda yadda zabe ke tafiya wajen kula da yadda ake zabe ba.”

Young yayi wa INEC tabbacin cewa za su bada goyon bayan tabbatar da an gudanar da zabe sahihi.

Ya kai ziyarar ce tare da wakilan Kungiyar Tarayyar Turai (EU) da na jakadancin Faransa da Jamus.

Ya kuma yi fatan sabon Sufeto Janar na ‘yan sanda, Adamu Mohammed zai yi aiki tukuru, ba tare da ya bari jami’an sa sun bata rawar su da tsalle ba.

Shi kuma Karlsen Ketil na EU, ya shaida wa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu cewa ya je ne domin ya ji kuma ya ga irin shirye-shiryen da INEC ta yi wajen tunkarar zaben tunda aski ya rigaya ya zo gaban goshi.

Yakubu ya ce ana nan ana ci gaba da kawo kayan aiki, ana ci gaba da tsare-tsare.

Ya sake yi musu alwashin cewa INEC ba za ta ba Najeriya da duniya kunya ba.

Share.

game da Author