Za mu hada hannu da ma’aikatan jinya domin raya fannin kiwon lafiyar kasar nan- Kungiyar Likitocin Najeriya

0

Shugaban kungiyar likitocin najeriya (NMA) Francis Faduyile ya bayyana cewa a dalilin hadin kai da samun daidaituwa a tsakanin kungiyar Likitoci da na ma’aikatan jinya fannin kiwon lafiyar Najeriya zai samu ci gaba matuka.

Idan ba a manta ba likitocin Najeriya da na ma’aikatan jinya sun dade basa ga maciji a tsakanin su a dalilin ko waye yafi mahimmanci ga fannin kiwon lafiya.

Rikicin ya kaida har suka soke juna suna jifar juna da muggan kalamai a bisa sana’ar su.

Faduyile ya ce yanzu komai ya zama tarihi cewa wannan matsala ba shi kuma. Suna tare sannan sun amince da kokarin kowannen su wajen ganin an samu ci gaba a fannin kiwon lafiya.

” Hakan zai kara sa a samu kiwon lafiya mai nagarta a asibitocin kasar nan.

Share.

game da Author