Gwamnatin tarayyata zata karbi bakuncin babban taron kawar da cutar zazzabin Lasa na karon farko a Abuja.
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ce za ta jagoranci shirya taron sannan taron zai gudana ne daga ranar 16 zuwa 17 ga watan Janairun 2019.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa ma’aikatan kiwon lafiya daga kasashen duniya za su halarci taron domin tattauna hanyoyin dakile yaduwar cutar a yankin yammacin Afrika.
” Taron zai tattauna inganta matakan hana yaduwar cutar musamman a tsakanin beraye da mutum da tsakanin mutum da mutum kuma.
” Za kuma a tattauna hanyoyin hassafa bincike game da cutar tare da sarrafa ingantatun magungunan cutar.
Ihekweazu ya ce ya zama dole yankin yammacin Afrika ta mike tsaye cak domin ganin an kau da wannan cuta cikin gaggawa.
Ya bayyana cewa a 2018 cutar ya yi ajalin mutane 146 kuma mutane 581 na dauke da cutar a Najeriya.
” Bayan shekaru 50 da bullowar wannan cutar a jihar Barno, Najeriya a 2018 ne kadai cutar ta yi ajalin mutane da dama.
A dalilin haka yake kira ga kasashen yammacin Afrika da su hada hannu domin ganin an kawar da cutar.
Discussion about this post