Za a fara atisayin ‘Operation Python Dance’ a jihar FIlato

0

Runduanar sojin Najeriya ta bayyana cewa sojoji za su fara atisayin ‘Operation Python Dance’ a jihar Filato.

Jami’in rundunar Nuhu Angbaza ya sanar da haka inda ya kara da cewa za a fara atisayin ne ranar 28 ga watan Disamba zuwa ranar 28 ga watan Faburairu a kauyukan Rafiki da Dutse Kura dake karamar hukumar Bassa a jihar.

Angbaza ya bayyana cewa rundunar ta amince da yin haka ne domin ta samarwa mutane da dukiyoyin su tsaro a yanzu da kuma bayan an gudanar da zaben a 2019.

Ya ce rundunar za ta hada hannu da sauran jami’an tsaron dake kasar musamman na jihohin Filato, Bauchi, Gombe, Adamawa da Taraba domin samaun nasara akai.

” Za mu fi bada karfi ne wajen ganin mun dakile munanan aiyukka a kasar nan ta hanyar kare rayukan mutane da dukiyoyin su kuma a kasan.

A karshe yayin da yake jinjina aiyukkan samar da tsaron da rundunar sojin Najeriya ke shirin yi gwamnan jihar Filato Simon Lalong yace yana kyautata cewa hakan zai samar da tsaro a duk fadin kasar nan.

Share.

game da Author