Wasu kwararrun ma’aikatan fannin kiwon lafiya sun yi kira ga kasashen Afrika da su mai da hankulan su wajen ganin sun inganta yin allurar rigakafi a kasashen su.
Kwararrun sun yi wannan kira ne a taron inganta yin allurar rigakafi wanda kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) na yankin kasashen Afrika ta yamma ta shirya.
Shugaban taron Helen Rees ta ce bincike ya nuna cewa yin allurar rigakafi a kasashen Afrika na nan a kashi 72 bisa 100 shekaru biyar da suka gabata.
Rees ta ce a dalilin haka cututtukan da za a iya kawar da su ta hanyar yin allurar rigakafi na nan na kisan yara kananan musamman ‘yan kasa da shekara biyar.
Ta ce za a iya shawo kan wannan matsala ne idan ana wayar da kan mutane musamman mazauna karkara game da mahimmancin yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gidauniyyar Bill da Melinda Gates ta tallafa wa fannin kiwon lafiyar Najeriya da dala miliyan 75.
Jam’in gidauniyyar Paul Bassainga ya sanar da haka a taron shirin tallafa wa jihohin da suka nuna himma wajen inganta fannin kiwon lafiyar su da aka yi a Abuja.
Bassainga ya jinjina wa kokarin da gwamnatin Najeriya ta yi a bangaren yin allurar rigakafi inda hakan ya sa gidauniyar za ta bata wannan tallafawa
Discussion about this post