Yawan shan zaki na haddasa cutar hanta – Bincike

0

Wasu masu bincike a kasar Amurka sun yi kira ga mutane da su guji yawan shan kayan zaki.

Masu binciken sun bayyana cewa lallai yawan haka na haddasa cutar hanta.

Shi dai wannan bincike anyi shi wa musamman mutane masu bakin fata dake kasar Amurka.

Sakamakon binciken ya nuna cewa cutar hanta na kama tsofaffin da suke yawaita shan zake a lokacin da suke da kurucciya.

A dalilin haka wadannan masu binciken suke kira ga matasa da su rage yawan shan zaki domin guje wa kamuwa da cutar hanta a musamman lokacin da suka tsufa.

Share.

game da Author