A yau ne tsohon dan wasan Real Madrid, Christiano Ronaldo, zai gurfana a gaban kotun kasar Spain domin ya amsa laifin sa na kin biyan harajin wasu kwangilolin talla da ya yi wa wasu kamfanoni.
Ana sa ran Ronaldo zai amince da aikata laifin dominn a kawo karshen wannan tirka-tirka da ta dade, tun a lokacin da ya ke wasa a kungiyar Real Madrid ta kasar Spain.
Domin kauce wa dauri, Ronaldo zai biya zunzurutun kudi har dalar Amurka milyan 21, kwatankwacin Fam milyan 17 na Ingila, sannan kuma daidai da naira bilyan bakwai da miliyan dari shida da sittin a biyar na kudin Najeriya, (wato N7, 665, 000,000.00).
Ronaldo zai halarci kotunn ne daga sabon gidan sa da ya saya a birnin Turin, a Italy, inda a yanzu ya ke buga wa kungiyar Juventus ta birnin Turin wasa.
Ana zargin Ronaldo da laifin damfarar gwamnatin Spain wajen kin biyan haraji tsakanin shekarun 2011 har zuwa 2014, a wasu talloli da ya yi wa wasu kamfanonin kasashen waje da ba na cikin kasar Spain ba.
Tun cikin 2017 aka fara wannan bibiyar shari’a, inda Ronaldo ya yi ta jaddada cewa shi bai yi wani laifi ba.
Amma a karshe ya sasanta tare da masu gabatar da kara cewa ya amince zai biya dala milyan 21 a matsayin tara da kuma cikon kudin harajin da bai biya ba din duk su na cikin wannan adadi.
Yin haka alama ce da ke nuna cewa idan aka ci gaba da shari’a, har aka tabbatar da cewa Ronaldo ya aikata laifin, to sai ya yi zaman wa’adi a gidan bursuna.
Jaridar The Independent ta Landan ta ruwaito cewa ba wani zama za a yi a kotun a dade ba.
Kawai za a tambayi Ronaldo ne, a ce masa ‘Shin ka aikata laifin ko ba ka aikata ba?’
Da zarar ya ce, “Na aikata”, to shikenan, tunda bai wahalar da kotu ba, sai a ce to ya biya tarar dala milyan 21, kwatankwacinn sama da naira bilyan bakwai da rabi kenan, sai a wuce wurin.
WASU YAN WASA DA AKA TABA CIN SU TARAR KIN BIYAN HARAJI
Ba kan Ronaldo farau ba. Akwai fitattun ‘yan wasa har 30 da a baya aka taba cin su tara, ciki kuwa har da Cristiano Ronaldo da aka ci tarar dala milyan 5.1 tare kuma da biyan kudin ruwa na tarar har dala milyan 1.
An taba cin David Beckham tara, an ci Lionel Messi, Xabi Alonso da sauran su da dama.