Rundunar ‘Yan sandan Jihar Katsina ta bada sanarwar kashe wani kasurgumin dan fashi da makami, mai suna Kane Mohammed, wanda aka fi sani da lakabin ‘Dan Maikeke’.
Sun ce dan fashin mai shekaru kimanin 35, ya dade a cikin jerin sunayen wadanda jami’an su ke nema ruwa a jallo.
Wannan bayanin ya na cikin wata takarda da kakakin yada labarai na rundunar ta Katsina, Gambo Isa ya fitar ga manema labarai a jiya Lahadi a Katsina.
Isa ya ce an bindige Dan Maikeke a garin Bakori, bayan da ‘yan sanda suka cim masa a mabuyar sa da ke Tsohuwar Kasuwa, a ranar 4 Ga Janairu.
Ya ce ‘yan daba din ne suka fara kai wa ‘yan sanda hari inda har suka ji wa wasu daga cikin su ciwo.
“Yan sanda inji shi sun harbe Dan Maikeke, wanda shi ne gogarman su. Sai dai kuma ya mutu a asibitin Bakori, sanadiyyar ciwon da aka ji masa.
Ya ce ’yan sanda sun dade su na neman sa, saboda yadda ya fitini al’ummar garin Bakori da Funtua da yawan fashi.
Daga nan ya ce ana ci gaba da binciken yadda za a kamo sauran ragowar gungun ‘yan fashin da ke karkashin Danmaikeke.