‘Yan sanda sun kama mai gadin da ya ci mutuncin ‘ya shekara 4

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Akwa Ibom Musa Kimo ya bayyana cewa sun kama wani mai gadin cocin ‘Royal City Central Chapel’ dake Uyo Joseph Effiong da laifin yi wa ‘yar shekara hudu fyade.

Kimo ya fadi haka ne wa manema labarai a garin Uyo inda ya kara da cewa Effiong mai shekaru 29 ya aikata wannan ta’asa ne ranar 13 ga watan Janairu.

Ya ce Effiong ya dane wannan yarinya ce a kangon gini dake kusa da cocin bayan lallabarta da yayi ya kai ta wannan wuri.

Bayan haka Kimo ya kuma ce rundunar ta sake kama wani magidanci mai suna Joseph Sunday Essien da laifin yi wa agolar gidan sa mai shekaru 13 fyade.

Har ila yau dan sandan ya ce sun kama wani Edet Inyang Edem kuma da laifin yi wa ‘yar shekara goma fyade inda bayan ya aikata ta’asar ne sai ya ajiye yarinyar a bakin kasuwa a garin Uyo.

Kimo yace da zaran sun kammala gudanr da bincike za a gurfanar da su a kotu.

Yace rundunar za ta ci gaba da kokari wajen ganin ta kare rayuka da dukiyoyin mutane a jihar.

Share.

game da Author