‘Yan sanda sanye da badda kama sun waske da Dino daga Asibiti

0

‘Yan sanda sanye da badda kama a fuskokin su sun dira asibitin da sanatan Dino Melaye ke kwance inda suka waske da shi da karfin tsiya.

Kamar yadda rahotanni ya iske PREMIUM TIMES, Ko motar da aka saka shi ciki ma a rufe take didum babu ko lamba a jiki.

Sun tafi da shi wani wuri ne da babu wanda ya san inda suka tafi dashi.

Idan ba a manta ba sai da akayi wajen kwanaki bakwai ana farautar sanata Dino a gidan sa inda daga baya ya fito da kan sa ya mika kan sa ga ‘yan sanda.

Tun daga wancan lokacin Dino ke kwance a wani Asibiti mallakar rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Ana zargin sanata Dino da hannu a harbe wani dan sanda mai suna Salihu a jihar Kogi.

Share.

game da Author