Wani gungun ‘yan daba sun kai hari rukunin gidajen iyalan Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki a cikin Ilorin, Babban Birnin Jihar Kwara.
Daya daga cikin hadiman sa na harkokin kafafen sadarwa, ya ce sun ji wa mutane 11 rauni kuma sun lalata motocin da suka kai 50.
Olu Onemola, ya kara da cewa ‘yan dabar duk magoya bayannjam’iyyar APC ne.
Wasu hotuna da Onemola ya turo wa PREMIUM TIMES, sun nuna yadda aka ragargaza gilasan wasu motoci.
Wannan farmaki ya zo ne kwanaki kadan bayan da Saraki ya sanar da cewa ana kulle-kullen kai wa magoya bayan sa hari.
Dama tun a ranar Juma’a sai da Saraki ya gaya wa manema labarai cewa ‘yan sanda na bada kariya ga masu kai wa magoya bayan sa hari.
Saraki ya ce da daurin gindin DPO na yankin Adewole aka kai wa gidan iyalin sa harin da misalin karfe 11:30 na safiya.
“Cikin motocin da aka lalata har da ta Liman Aliagan, kuma an gudu da babaura hudu, an sacin kudade da kayan gwala-gwalai daga cikin kantunan da masu tsaron su suka gudu domin tsira daga harin ’yan daba.’’